Isa ga babban shafi
Champions League

Za’a hada kungiyoyin da za su kara a zagaye na biyu

A gobe Alhamis ne za’a hada kungiyoyin da za su kara da juna a gasar zakarun Turai zagaye na biyu a kasar Switzerland wadanda ke naman shiga filin wasa na Wembley a wasan karshe da za’a gudanar a ranar 25 ga watan Mayun badi.

Tanbarin Gasar Zakarun Turai
Tanbarin Gasar Zakarun Turai
Talla

A bana dai wata kungiya ce za ta daga kofin, bayan Chelsea ta kasance kungiya ta farko mai rike da kofin gasar da ta fice tun a zagayen farko.

A watan Fabrairu ne za’a dawo fagen daga, kuma manyan kungiyoyi irinsu Manchester United da Paris Saint-Germain da Borussia Dortmund da Malaga da Juventus da Schalke 04 da kuma Bayern Munich yana da wahala su hadu da Barcelona kungiyar da ake wa kallo daya daga cikin masu iya lashe kofin gasar domin sun kasance na daya a Teburisu a zagayen Farko.

Haka kuma Real Madrid da ta lashe kofin gasar sau Tara ba zai yiyu ta hadu da abokiyar hammayarta ta ba Barcelona a zagaye na biyu domin a tsarin gasar kungiyoyi daga kasa daya ba za su hadu da juna ba sai a zagayen quarter final.

Akwai dai yiyuwar Bayern Munich ta kasar Jamus za ta iya haduwa da Real Madrid ko Celtic ko Porto ko Shakhtar ko Arsenal.

Kungiyoyi irinsu Manchester United da Juventus da Borussia Dortmund suna cikin kungiyoyin da ko wace kungiyar za ta nemi ta kaucewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.