Isa ga babban shafi
Champions League

Chelsea ta fice, Messi zai yi jinya

A gasar Zakarun Turai kungiyar Chelsea mai rike da kofin gasar ta fice duk da ta lallasa FC Nordsjaelland ci 6-1 a wasan karshe da aka gundanar a rukunin farko. Duk da kwallayen da Fernando Torres da David Luiz da Gary Cahil da Juan Mata da Oscar suka zira a raga sun zama duk a banza domin Juventus ta doke Shakhtar Donetsk ci 1-0 wanda hakan ya haramtawa Chelsea tsallakewa.

Dan wasan Chelsea, Fernando Torres.
Dan wasan Chelsea, Fernando Torres. REUTERS/Dylan Martinez
Talla

Sai dai kuma Rafeal Benitez wannan ne karon farko da ya samu nasarar wasa a wasanni hudu da ya jagoranci Chelsea a matsayin koci bayan Sallamar Di Matteo.

Yanzu dai Chelsea za ta garzaya ne zuwa gasar Turai ta Europa, domin ita ce ta uku a teburin rukuninsu.

Kungiyar Celtic kuma ta Scotland ta tsallake zagaye na biyu bayan ta doke Spartak Moscow ci 2-1. Kuma ta samu karin gwiwa ne saboda an tashi wasa babu ci tsakanin Barcelona da Benfica.

A wasan Barcelona da Benfica ne dai Lionel Messi ya samu rauni a gwiwa, kuma kungiyar Bercelona ta sanar a shafinta na Intanet cewa dan wasan ya gurje ne kawai a gwiwar shi ta hagu, kuma dan wasan yanzu yana jiran likitoci su sake gwada shi domin tantance lokacin da zai kwashe kafin ya samu sauki.

Babu dai tarihi da Messi ya kafa domin yin kafada da Mueller a matsayin wanda ya fi kowa zira kwallaye a raga a kakar wasa.

Kungiyar Galatasaray ma ta tsallake zagaye na gaba bayan samun nasarar doke Braga ci 2-1. Amma Manchester United duk da ta tsallake, a jiya kungiyar Cluj ta samu a’ar doke United ci 1-0 a Old Trafford

A jiya ne dai Sir Alex Ferguson ya haska karo na 200 a gasar zakarun Turai a matsayin kocin Manchester.

Kuma Ferguson yace galabarsu da aka samu a daren jiya ba zai karya masu gwiwa ba a wasan da za su kece riani da Manchester City a karshen mako.

Bayern Munich kuma ta lallasa BATE Borisonv ne ta Belarus ci 4-1, kamar yadda Valencia tabi Lille har gida ta doke ta ci 1-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.