Isa ga babban shafi
Champions League

City ta fice, Arsenal da PSG da Madrid sun tsallake

Kungiyar Manchester City ta fice gasar Zakarun Turai bayan ta yi kunnen doki da Real Madrid a wasan Mourinho kocin Madrid ya haska sau 100 a gasar. Yanzu Kungiyoyin 13 ne dai yanzu suka tsallake saura kungiyoyi guda Uku.

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya dahe baki a wasa tsakaninsu da Ajax
Kocin Manchester City Roberto Mancini ya dahe baki a wasa tsakaninsu da Ajax REUTERS/Darren Staples
Talla

Kungiyoyin da suka tsallake sun hada da AC Milan, da Arsenal da Barcelona da Bayern Munich da Borussia Dortmund da Malaga da Manchester United da Paris Saint Germain da Porto da Real Madrid da Schalke 04 da Shakhtar Donetsk da kuma Valencia.

Borussia Dortmund dai ta lallasa Ajax ne ci 4-1 a Amsterdam. Kuma Dortmund ce ta jagoranci Rukuninsu na D da tazarar maki 3 tsakaninta da Real Madrid.

Olympiakos dai ta sha kashi ne hannun Schalke 04 ci 1-0 yayin da kuma Arsenal ta doke Montpiller ci 2-0 a Rukuninsu na B.

PSG kuma ta tsallake ne bayan doke Dynamo Kiev ci 2-0 a Ukraine. PSG ta samu damar tsallakewa ne da maki 12 yayin da kuma FC Porto ta jagoranci Rukuninsu da maki 13 bayan ta lallasa Dinamo Zagreb ci 3-0.

Roberto Mancini kocin Manchester City ya amsa samun kura kura amma yace yanzo fatan shi ita ce shiga gasar Europa da kafar dama. Sai dai wasu suna hasashen Mancini na iya bin sahun Di Matteo da aka kora saboda rashin dadin sakamakon wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.