Isa ga babban shafi
Champions League

Chelsea ta sha kashi, Barcelona da Munich sun tsallake

Barcelona da Bayern Munich sun tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai amma Chelsea mai rike da kofin gasar ta fada tarko domin za ta iya kasancewa kungiya ta farko mai rike da kofin gasar da za ta fice tun a zagayen farko bayan ta sha kashi hannun Juventus.

Mai tsaron gidan Chelsea Petr Cech yana nuna bacin rai bayan Juventus ta zira kwallaye Uku a ragar shi a gasar Zakarun Turai
Mai tsaron gidan Chelsea Petr Cech yana nuna bacin rai bayan Juventus ta zira kwallaye Uku a ragar shi a gasar Zakarun Turai REUTERS/Tony Gentile
Talla

Sauran kungiyoyin da suka tsallake a zagaye na gaba sun hada da Valencia da Shakhtar Donetsk, kungiyar Celtic kuma akwai sauran aiki a gabanta domin ta sha kashi ne a hannun Benfica.

Chelsea mai rike da kofin gasar dai ta sha kashi ne a gidan Juventus ci 3-0, wanda yasa kuma Chelsea ta koma matsayi na uku a Teburin Rukuninsu.

Shakhtar Donetsk dai ta lallasa Nordsjaelland ci 5-2.

Barcelona kuma tabi Spartak Moscow ne har gida ta zira mata kwallaye 3 a raga wannan nasarar ce kuma ta ba Barcelona damar tsallakewa zagaye na gaba.

Messi dai shi ne ya zira kwallaye biyu, bayan Dani Alves ya zira kwallon farko.

Yanzu haka kuma Lionel Messi yana kafada ne da Ruud van Nistelrooy da kwallaye 56 a raga a tarihin zira kwallo a gasar zakarun Turai. Messi dai yana neman kamo kafar Raul ne tsohon dan Wasan Real Madrid wanda ke da yawan kwallaye 71 a raga a tarihin gasar Zakarun Turai.

Wasa tsakanin Velencia kuma da Bayern Munich an tashi ne kunnen doki ci 1-1 wanda ya ba kungiyoyin biyu damar tsallakewa zuwa zagaye na biyu bayan Lille ta Faransa ta doke Bate Barisov ci 2-0.

A birnin Istanbul kuma Galatasaray ta karya lagon Manchester United bayan ta doke ta ci 1-0. Tuni dai Manchester United din ta tsallake a zagaye na gaba.

A yau Laraba kuma akwai wasan kece raini tsakanin Mourinho da Mincini inda Real Madrid zata kara da Manchester City.

Yana da wahala dai City ta kwaci kanta hannun Madrid domin Real Madrid ce ke jagorancin Rukuninsu, sannan a karawar farko ‘Yan wasan Mourinho sun lallasa Mancini ci 3-2 a Bernabeur.

Manchester City dai tana kan hanyar Ficewa gasar ne amma a yau tana neman samun galabar Real Madrid tare da fatar doke Borussia Dortmund a nan gaba kafin ta samu damar tsallakewa a zagaye na biyu.

Sai dai kuma Mourinho yace ko City ta samu galabar shi a yau Laraba, ya yi imanin sai ta fice daga gasar.

Akwai sauran wasanni kamar Haka:

Porto da Dinamo Zagreb

Dynamo Kiev da Paris Saint Germain

Arsenal da Montpellier

Schalke da Olympiakos

Zenit St Petersburg da Malaga

Ajax da Borussia Dortmund
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.