Isa ga babban shafi
Champions League

Juventus da Chelsea za su kece raini, Bayern za ta kara da Valencia

Kungiyoyin Birtaniya guda biyu, Chelsea ta Ingila Mai rike da kofin Gasar Zakarun Turai da Celtic ta Scotland za su nemi tsallakewa zuwa zagaye na biyu idan sun maimaita kokarin da suka yi a makwanni biyu da suka gabata.

Tambarin gasar Zakarun Turai
Tambarin gasar Zakarun Turai
Talla

Kungiyar Chelsea dai za ta kai ziyara ne Italiya domin karawa da Juventus. Cetltic kuma sai ta yi da gaske domin za ta kara ne da Benfica da ke neman tsallakewa, bayan Celtic din ta samu nasarar doke Barcelona ci 2-1 a wasannin da suka gabata.

Bayern Munich kuma za ta kai ziyara ne Spain domin karawa da Valencia, inda za’a maimaita tarinhin wasan karshe tsakanin kungiyoyin biyu a shekarar 2001.

Bayern dai da Valencia dukkaninsu suna jayayyar Teburin Rukuninsu ne da maki Tara Tara, amma suna fuskantar matsin lamba ne daga Bate Barisov wacce ke da maki Shida a matsayi na uku, kuma za ta iya ba su mamaki idan ta doke lille da ke matsayi na Karshe.

Valencia ko Bayern Duk kungiyar da ta lashe wasan yau zai kasance ta tsallake zuwa zagaye na biyu.

A makwanni biyu da suka gabata Chelsea ta sha da kyar ne hannun Shakhtar Donetsk, amma a karshen mako Chelsea ta sha kashi a Premier hannun West Brom Albion. A yau kuma yan wasan Di Matteo suna da babban aiki a gabansu inda za’a yi wasan iya warka ta fitar da kai tsakanin Chelsea da Juventus.

Chelsea dai za ta fuskanci barazana idan har ta yi barin maki uku a gidan Juventus, Domin juventus za ta nemi lallasa Chelsea.

Kungiyar Barcelona ta Spain kuma za ta nemi tsallakewa ne a yau Talata inda za ta kai wa Spatak Moscow Ziyara a Rasha, bayan Barcelona ta sha kashi a hannun Celtic a wasannin da suka gabata wanda ya hana ta kammala aikinta.

A Birnin Copenhagen kawai wasa tsakanin Nordsjaelland ta Denmark da v Shakhtar Donetsk Ukraine

A birnin Istanbul, Galatasaray ce zata fafata da Manchester United wacce tuni ta tsallake a zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.