Isa ga babban shafi
Champions League

Tarko ya kama City, Madrid da Arsenal sun sha da kyar

Tarkon da Manchester City ta fada ya kamata domin yana da wahala ta tsallake bayan an tashi wasa ci 2-2 tsakaninta da Ajax. Real Madrid da Arsenal dukkaninsu sun sha da kyar ne domin an tashi wasanninsu ci 2-2.

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya dahe baki a wasa tsakaninsu da Ajax
Kocin Manchester City Roberto Mancini ya dahe baki a wasa tsakaninsu da Ajax REUTERS/Darren Staples
Talla

Saura kada ne dai Borussia Dortmund ta yi wa Madrid gida da waje, amma Mesut Ozil ne ya kwato ‘Yan wasan Mourinho ana mintinan karshe a tashi wasa wanda ya zira kwallo ta biyu da ya sa aka tashi wasan ci 2-2.

Har yanzu dai Borussia Dortmund dai Ce ke jagorancin Rukunin da maki 8, Real Madrid ce a matsayi na biyu da maki 5, Ajax ce a matsayi na uku da maki 4. Manchester City ce ta karshe da daya.

Akan haka ne kuma Roberto Mancini yace sun fice gasar.

Kungiyar Arsenal kuma ta yi barin maki uku inda ‘Yan wasan Arsene Wenger suka bari Schalke 04 ta barke kwallye biyu da suka fara zirawa a ragarsu.

A rukuninsu na B, kungiyar Schalke 04 ce ke jagorancin Tebur da maki 8, tazarar maki daya tsakaninta da Arsenal. Kungiyar Olympiakos ce ta kasar Girka a matsayi na biyu wacce ta lallasa Montpellier ta karshe ci 3-1.

Kungiyar Malaga kuma ta yi kunnen doki ne ci 1-1 da AC Milan. Kuma hakan ke nuna Malaga ta tsallake a zagaye na gaba.

Makwanni biyu da suka gabata Malaga ta doke Milan ci ci-1-0.

A Rukunin A, an tashi wasa ne babu ce tsakanin Dynamo Kiev ta Ukriane da FC Porto Portugal. A birnin kuma Paris Saint-Germain ta lallasa Dinamo Zagreb 4-0.

A yau kuma ne kuma Manchester United za ta kara da Braga, Chelsea kuma mai rike de kofin gasar za ta nemi rama kashin da ta sha ne hannun Shakhtar Donetsk. A daya bangaren Kungiyar Celtic za ta karbi bakuncin Barcelona ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.