Isa ga babban shafi
Champions League

Arsenal da City da Madrid da Milan za su nemi rama kashin da suka sha

Kungiyoyin Ingila guda biyu Arsenal da Manchester City za su nemi rama kashin da suka sha a wasannin da suka gabata a gasar Zakarun Turai. Haka kuma Real Madrid da AC Milan za su nemi rama kashin da suka sha hannun Borussia Dortmund da Malaga.

José Mourinho. kocin Real Madrid a spain
José Mourinho. kocin Real Madrid a spain ©Reuters
Talla

Idan dai har City ta sake shan kashi hannun Ajax  zai kasance hanyar ficewar kungiyar daga gasar a bana. Hakan kuma wani kalubale ne ga Roberto Mancini.

Kodayake Mancini zai yi fatar a ta shi wasa babu ci tsakanin Real Madrid da Borussia Dortmund.

Dortmund ce dai ke jagorancin Rukuninsu da maki Bakwai, tazarar maki daya tsakaninta da Real Madrid, kungiyar Manchester City ce ta karshe a Rukuninsu bayan buga wasanni uku.

Mourinho dai yana neman lashe kofin gasar zakarun Turai a kungiyoyi uku a kasashe daban daban. Kuma a yau Talata zai kara ne Dortmund bayan ya lallasa Real Zaragoza ci 4-0 a La liga.

Kungiyar Arsenal kuma za ta kai wa Schalke 04 ziyara ne a kasar Jamus bayan ta sha kashi a wasannin da suka gabata. Amma sai Arsene Wenger ya yi da gaske saboda Olympiakos na iya doke Montpellier ta Faransa.

A daya bangaren kuma, FC Porto za ta kai wa Dynamo Kiev ziyara ne yayin da kuma AC Milan za ta karbi bakuncin Malaga.

A makwanni biyu da suka gabata AC Milan ba ta sha dadi ba a gidan Malaga domin ta sha kashi ci 1-0.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.