Cheslea ta sha kashi, Barcelona da United sun sha da kyar
Chelsea mai rike da kofin gasar zakarun Turai ta sha kashi hannun Shakhtar Donetsk a Ukraine ci 2-1, Barcelona da Manchester United kuma sun sha da kyar, amma Bayern Munich ta doke Lille ci 1-0. Roberto Saldado ya zira kwallaye uku a ragar Bate Barisov.
Wallafawa ranar:
Wasa tsakanin Barcelona da Celtic a Nou Camp an ta shi ne ci 2-1. Dan wasan Barcelona ne Javier Mascherano ne ya fara cin kansu inda ya zira kwallon a ragar Barcelona, ana gab da zuwa hutun rabin lokaci ne kuma Andres Iniesta ya barke kwallon a ragar Celtic. Ana mintinina karshe kuma Jordi Alba ya sake zira kwallon da ya ba Barcelona nasara akan Celtic.
Javi Hernandez da Jonny Evans ne suka ceto Manchester United a Old Trafford bayan dan wasan Braga Alan ya zira kwallaye biyu a raga.
Kungiyar Chelsea kuma sai ta yi da gaske kafin ta tsallake zagaye na biyu bayan ta sha kashi a gidan Shakhtar Donetsk ci 2-1.
Kungiyar Shakhtar Donetsk ce ke jagorancin rukuninsu da maki 7, kuma kungiyar Juventus ce za ta iya haramtawa Chelsea tsallakewa wacce ta yi kunnen doki a Copenhagen ci 1-1 da Norjaelland.
Kocin Chelsea Roberto Di Matteo yace ‘Yan wasan shi za su rama kashin da suka sha idan Shakhtar Donetsk ta kawo ma su ziyara a Stamford Bridge.
A gidan Lille kuma Bayern Munich ta doke ta ci 1-0 a bugun daga kai sai mai tsaron gida da Thomas Mueller ya zira a ragar Lille.
Dan wasan Valencia kuma Roberto Soldado a jiya kwallaye uku ya zira a ragar Bate Barisov ta Belarus.
Spartak Moscow kuma ta Rasha ta samu galabar Benfica ci 2-1 a birnin Moscow. Kuma wannan ce nasara ta farko da Spertak ta samu tun fara gasar Zakarun Turai a bana.
A yau ne kuma Real Madrid ta Spain za ta bakunci Borussia Dortmund a kasar Jamus, kamar yadda Ajax zata karbi bakuncin Manchester City ta Ingila.
Yan wasan Gunners kuma za su kara ne da Schalke a filin wasa na Emirates. ‘Yan wasan Arsene Wenger dai za su yi kokarin huce kashin da suka sha ne a karshen mako hannun Norwich.
Kungiyar Malaga kuma ta Spain za ta karbi bakuncin AC Milan. A Croatia, Dinamo Zagreb za ta fafata da Paris Saint Germain ta Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu