Isa ga babban shafi
Champions League

Celtic ta doke Barcelona, Chelsea ta kwaci kanta hannun Donetsk

A birnin Glasgow kasar Scotland Celtic ta doke Barcelona ci 2-1, yayin da kuma Chelsea ta kwaci kanta a mintinan karshe. Manchester United kuma ita ce kungiya ta uku yanzu da ta samu nasarar tsallakewa zagayen na biyu a gasar Zakarun Turai bayan doke Braga ci 3-1.

'Yan wasan Chelsea Victor Moses  John Obi Mikel dukkaninsu 'Yan Najeriya suna murnar kwallon da Mosses ya zira a ragar Shakhtar Donetsk a Stamford Bridge
'Yan wasan Chelsea Victor Moses John Obi Mikel dukkaninsu 'Yan Najeriya suna murnar kwallon da Mosses ya zira a ragar Shakhtar Donetsk a Stamford Bridge REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Barcelona dai ta yi ta kai hare hare amma kuma Celtic ce ta samu sa’ar zira kwallaye a raga. Ana mintininan karshe ne Messi ya samu ya zira kwallo daya bayan Victor Wanyama da Tony Watt sun zira kwallaye biyu a ragar Barcelona inda aka tashi wasan ci 2-1

Nasarar da Celtic ta samu akan Barcelona na zuwa kwana daya bayan kungiyar ta cika shekaru 125 da kafawa.

Kungiyar Chelsea kuma mai rike da kofin gasar da kyar ta kwaci kanta daga hannun Shakhtar Donetsk a Stamford Bridge.

Dan wasan Najeriya Victor Mosses shi ne ya zira kwallon karshe da aka tashi wasan ci 3-2. Yanzu kuma Chelsea tana a matsayi na biyu ne a Teburin rukuninsu da maki Bakwai makinta daya da Shakhtar Donetsk da ke jagorancin Teburin da yawan kwallaye.

Juventus ce a matsayi na uku da maki Shida wacce ta lallasa Nordsjaelland ci 4-0.
Chelsea kuma sai ta yi da gaske domin a ranar 20 ga Watan Nuwamba ne zata san matsayinta inda zata kara da Juventus.

Kungiyar da ta kwashi garabasar kwallye a daren jiya, ita ce Bayern Munich inda Pizarro ya zira kwallye uku cikin kwallaye Shida da Bayern Munich ta zira a ragar Lille.
Bayern Munich dai tana jayyaya ne tsakaninta da Velencia a rukuninsu, domin Valencia ma a daren jiya ta doke Bate Borisov ci 4-2.

Bayern da Valencia dukkaninsu suna da maki Tara-Tara ne yayinda Bate ke a matsayi na uku da maki Shida.

A birnin Lisbon na kasar Portugal, Benfica ta doke Spartak Moscow ci 2-0. Sai dai Barcelona ce ke jagorancin Teburin rukuninsu da maki Tara, kungiyar Celtic kuma a matsayi na biyu da maki 7. Benfica ce a matsayi na Uku da maki Hudu. Spatak Moscow a matsayi na karshe da maki Uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.