Isa ga babban shafi
Champions League

City ta fice kuma Arsenal ta sha kashi

Kungiyoyin Ingila guda biyu Manchester City da Arsenal sun sha kashi a gasar zakarun Turai da aka gudanar a daren jiya. Kuma Manchester City ta yi hasara biyu ne domin ta fice gasar zakarun Turai sannan kuma Borussia Dortmund ta haramta mata shiga gasar Europa League bayan doke ta ci 1-0.

Kwallon ban haushi da Dortmund ta zira a ragar Manchester City
Kwallon ban haushi da Dortmund ta zira a ragar Manchester City REUTERS/Ina Fassbender
Talla

Borussia Dortmund ce dai ta jagoranci Rukuninsu na D, amma Manchester City ce ta karshe a teburin rukuninsu.

Real Madrid ce dai a matsayi na biyu, kuma a daren jiya ta lallasa Ajax ci 4-1. Cristiano Ronaldo da Kaka da Callejon sune suka zirawa Real Madrid kwallayenta a raga.

A tarihin gasar dai Manchester City ita ce kungiya ta farko daga Ingila da ta fice gasar da yawan maki uku kacal a zagayen farko.

Olympiakos, ce kuma ta doke Arsenal ci 2-1, kuma wannan nasarar ce ta ba Olympiakos, damar tsallakewa zuwa gasar Europa League.

Kashin da Arsenal kuma ta sha shi yasa ta dawo matsayi na biyu a rukuninsu wanda hakan kuma barazana ce ga Arsenal din, domin za’a iya hada ta wasa da manyan kugiyoyi irinsu Barcelona da Dortmund da Bayern Munich ko Valencia a zagayen na biyu.

Schalke 04 ce dai ta jagoranci Rukuninsu Arsenal amma a daren jiya Schalke ta yi kunnen doki ne a gidan Montpellier ta Faransa.

Carlo Ancelotti kuma ya samu sa’ida bayan Paris Saint Germain ta doke Porto ci 2-1. Domin aikin horar da ‘yan wasan PSG yana neman ya kubuce wa Ancelotti ne bayan kungiyar ta sauko saman Teburin league din faransa zuwa matsayi na 4.

PSG dai ta tsallake kuma ita ce kungiyar da ta jagoranci rukunin A.

AC Milan kuma ta sha da kyar ne a gidan Zenit St Petersburg ci 1-0.

Wasa tsakanin Dinamo Zagreb da Dynamo Kiev an tashi ne kunnen doki ci 1-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.