Ibrahimovic ya zira kwallaye uku a ragar Valenciennes
Dan kasar Sweden Zlatan Ibrahimovic ya zira kwallaye uku a raga wanda ya ba PSG nasarar lallasa Valenciennes ci 4-0. Yanzu haka kuma Zlatan Ibrahimovic yana da jimillar kwallaye 17 a raga wadanda ya zira a league din kasar Faransa.
Wallafawa ranar:
Tazarar maki biyu ne kuma yanzu Lyon ta ba Paris Saint-Germain a teburin league din faransa.
Ibrahimovic wanda tsohon dan wasan Barcelona ne da AC Milan da kuma Inter Milan ana minti 29 da fara wasa ne ya fara bude raga. A bana dai dan wasan yana haskawa ne domin ya zira wata kwallo a ragar Ingila da ba’a taba zira irinta ba a duniya.
Wannan ne karo na shida dad an ke zira kwallaye fiye da daya a wasa a bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu