Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Chelsea da Arsenal sun sha kashi, Messi zai wuce Mueller

Saura kwallo daya kacal Messi ya kamo kafar Gerd Mueller a matsayin wanda ya fi kowa zira kwallo a raga a kakar wasa, domin a karshen mako Messi ya zira kwallaye Biyu cikin wadanda suka zirawa Barcelona kwallaye 5 a ragar Athletic Bilbao.

Kocin Chelsea Rafa Benitez ya ware hannaye yana magana da 'Yan wasan shi a lokacin da suka sha kashi hannun West Ham a wasan Premier
Kocin Chelsea Rafa Benitez ya ware hannaye yana magana da 'Yan wasan shi a lokacin da suka sha kashi hannun West Ham a wasan Premier REUTERS/Andrew Winning
Talla

Muller na Jamus shi ne wanda ya zira kwallaye 85 a raga a kakar wasan 1972. Kuma yanzu Messi na Argentina yana neman karya tarihin shi.

A karshen mako, Real Madrid kuma ta doke Makwabiciyarta ne Atletico Madrid ci 2-0. Wanda ya ba Real Madrid nasarar kwace maki Uku hannun atletico Madrid domin rage yawan makin da ke tsakaninsu a Teburin La liga.

Tazarar maki 11 ne dai Barcelona taba Real Madrid da ke a matsayi na uku kasan Atletico Madrid da ke a matsayi na biyu.

Faransa

A karshen mako, kungiyar Lyon ce ta dare Tebur bayan doke Montpelier mai rike da kofin league din kasar ci 1-0.

PSG kuma ta sha kashi ne hannun Nice ci 2-1 Kamar yadda Kungiyar Marseille ta kwaci kanta hannun Brest ci 2-1.

Ingila

Rafeal Benitez ya sha kashi a karshen mako a wasan da West Ham ta casa Chelsea ci 3-1.

Benitez wanda ya gaji Di Matteo ya buga wasanni uku ba tare da samun nasara ba. kuma yanzu tazarar maki 10 ne Manhcester United taba Chelsea a teburin Premier.

A karshen mako dai Manhcester United ta sha da kyar ne a hannun Reading ci 4-3.
Manchester city kuma da Everton sun yi kunnen doki ne ci 1-1.

Kungiyar Liverpool kuma ta hauro zuwa matsayi na 11 bayan samun nasarar doke Southampton ci 1-0

Kungiyar Arsenal kuma ta sha kashi ne a hannun Swansea ci 2-0. Dan wasan Swansea Michu shi ne ya zira kwallayen guda biyu

Jamus

A Bundesliga, wasa tsakanin Bayern Munich da Borussia Dortmund an tashi ne kunnen doki ci 1-1. Hakan ne kuma yanzu ya rage yawan makin Bayern Munich a Tebur zuwa maki 8.

Karo na hudu ke nan Bayern Munich ba ta samu galabar Borussia Dortmund ba. amma a karshen mako Toni Kroos shi ne ya fara zirawa Bayern kwallo a raga daga bisani kuma Mario na Dortmund ya barke kwallon.

Tazarar maki 11 ne Bayern ta ba Borussia Dortmund a teburin Bundesliga. Bayer Leverkusen ce a matsayi na biyu wacce ta doke Nuremberg ci 1-0.

Rasha

Kungiyar Anzhi Makhachkala ta doke CSKA Moscow ci 2-0, kuma wannan ne ya karya lagon CSKA Moscow a bana wacce ta buga wasanni bakwai ba tare da samun galabarta ba.

CSKA da Anzhi sune a saman Teburin Premier na kasar Rasha da maki 40 bayan buga wasanni 18.

Mai rike da kofin gasar Zenit St Petersburg ita ce matsayi na uku da maki 37.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.