Isa ga babban shafi

Gwamnatin Sojin Nijar ta bude iyakar da ke tsakaninta da Najeriya

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da bude iyakarta da Najeriya tun da misalin karfe 12 na tsakar daren jiya Alhamis, lamarin da zai dawo da hada-hada tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.

Shugaban mulkin sojin Nijar, Abdourahmane Tiani
Shugaban mulkin sojin Nijar, Abdourahmane Tiani © RTN
Talla

Tun a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata ne aka rufe kan iyakar biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa hambararren shugaban kasar Bazoum Mohammed.

Fiye da mako guda kenan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin bude kan iyakar da ke tsakanin kasashen biyu makwabtan juna, yayin da sojojin na Nijar suka ki cewa uffam kan matakin na Najeriya.

Kazalika shugaba Tinubu ya janye daukacin takunkuman karayar tattalin arzikin da Najeriya ta lafta wa Nijar.

Kan iyakar mai tazarar kilomita 1,600 ta ratsa jihohin arewacin Najeriya da suka hada da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina da Jigawa da Yobe da Borno.

A wani zama da ta gudanar a baya-bayan nan, kungiyar ECOWAS ta  amince da shirin cire wa kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea takunkuman da aka dora musu sakamakon juyin mulkin soji da aka samu a cikinsu.

Masharhanta sun bayyana cewa, janye takunkuman da aka lafta wa Nijar, zai kawo saukin rayuwa ga al'ummar kasar da ke fama da tsadar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.