Ana dakon hukuncin kotun Ecowas dangane da karar jagoran yan Adawar Nijar
Ranar talata 31 ga watan Mayu ne kotun tsarin mulkin kasa ta kungiyar kasashen Ecowas dake Abuja zata zartas da hukunci dangane da karar da jagoran yan adawa a Jamhuriyar Nijar Mahamane Ousmane, Shugaban jam’iyyar RDR Canji ya shigar.
Wallafawa ranar:
Shugaban jam’iyyar RDR Canji Mahamane Ousmane ya kalubalanci nasarar shugaban kasar Bazoum Mohammed dangane da sakamakon zaben shugabancin kasar na watan Fabarairun zagaye na biyu.
Jam’iyyar RDR Canji ta bayyana cewa an tafka magudi,inda take kalon jam’iyyar PNDS a matsayin wacce ta shirya haka,banda magudin an samu tashin hankali a wasu wurare.
Za a dai gudanar da wannan zama a Abuja dake birnin Tarryar Najeriya a karkashin shugabancin alkalai da suka hada da Edouard Amoako Asante,Dupe Atoki da Januaria Tavares Silva Moreira Costa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu