Isa ga babban shafi
Nijar

Jega ya ba hukumar Zaben Nijar shawarwari

Tsohon Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya kai ziyara Jamhuriyyar Nijar domin ba hukumar zaben kasar shawarwari kan inganta ayyukan zabe.

Tsohon Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega
Tsohon Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Ofishin jakadancin Amurka ne a Niamey  ya gayyaci Farfesa Jega domin taimakawa hukumar zaben Nijar da shawarwari dangane da yadda za a inganta zaben kasar.

A ranar 20 ga watan Maris ne hukumar zabe mai zaman kanta CENI zata shirya zaben shugaban kasa zagaye na biyu inda Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou zai fafata da Hama Amadou da ake tsare da shi.

Sai dai kuma ziyarar Jega na zuwa ne bayan gungun ‘Yan adawa sun sanar da matakin kauracewa zaben a zagaye na biyu saboda rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben farko.

Farfesa Jega ya gabatar da takarda a wani taron karawa juna sani kan zaben Nijar a birnin Yamai.

Jega ya shaidawa RFI Hausa cewa ya tattaunawa da hukumomi masu ruwa da tsaki ga sha’anin zabe tare da tattaunawa da hukumar CNDP da ke tabbatar da daidaituwa tsakanin ‘Yan siyasar kasar.

Sannan ya tattauna da hukumar zabe da bangaren gwamnati kan yadda za a shawo kan matsalolin zaben kasar kamar yadda ya samu nasarar gudanar da zabe ingantacce a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.