Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan adawa za su kauracewa zaben Nijar zagaye na biyu

Gungun Jam’iyyun adawa na COPA da ke goyon bayan takarar Hama Amadou sun sanar da kauracewa shiga zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 20 ga watan Maris.

Magoya bayan Hama Amadou da zai fafata da shugaba Mahamadou Issoufou a zagaye na biyu a zaben Nijar
Magoya bayan Hama Amadou da zai fafata da shugaba Mahamadou Issoufou a zagaye na biyu a zaben Nijar ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Sanarwar da ‘Yan adawar suka fitar na dauke ne da sa hannun Seini Oumarou tsohon Firaminista.

A cikin sanarwar, ‘Yan adawar sun bukaci dukannin wakilansu su janye daga Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta CENI tare da yin kira ga magoya bayansu su kauracewa zaben.

'Yan adawar sun fitar da sanarwar kauracewa zaben ne bayan kotun tsarin mulki ta kasa ta fitar da sakamakon zabe zagaye na farko wanda ya bai wa shugaba Mahamadou Issoufou damar sake karawa da Hama Amadou a zagaye na biyu.

Kakakin ‘Yan adawar Alhaji Mahamadou Dudu, ya shaidawa RFI Hausa cewa sun yanke shawarar kauracewa zaben ne saboda rashin gamsuwa da tsarin shi.

A cewar Alhaji Dudu Kotun tsarin mulki ta amince da sakamakon zaben ba tare da la’akari da korafe korafensu ba da kuma yadda har yanzu ake ci gaba da tsare dan takararsu Hama Amadou.

"Yadda hukumar zabe ta ja kafa wajen bayyana sakamako da kuma yadda kotun koli ta fito da sakamakon a cikin dare sabanin yadda aka saba, ya nuna ba gaskiya a ciki", a cewar Dudu.

Sai dai gwamnati ta ce za a yi zaben a zagaye na biyu tare da yin watsi da korafin na ‘Yan adawa.

Ministan cikin gidan Nijar Hassoumi Massaoudou ya ce ‘Yan adawar sun fahimci za su sha kaye ne shi ya sanya suka ce zasu fice zagaye na biyu.

Zaben ya shiga zagaye na biyu ne bayan Shugaba Mahamadou Issoufou na PNDS Tarayya ya samu kashi 48.43 na kuri’u yayin da kuma Hama Amadou na Moden/Lumana ya zo a matsayi na biyu da kashi 17.73.

‘Yan adawar na zargi gwamnati da tauye hakkin Hama Amadou na, wanda ake tsare da shi kan badakalar mallakar ‘ya’ya da aka yo fataucinsu daga Najeriya.

01:17

Alhaji Mahamadou Dudu na 'Yan adawar Nijar

Lydia Ado

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.