CENI ta yi watsi da zargin ‘Yan adawar Nijar
Hukumar zaben kasar Nijar mai zaman kanta CENI, ta yi watsi da zargin ‘yan adawa da suka ce ba za su amince da sakamakon zaben shugaban kasa saboda an yi magudi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kawo yanzu hukumar zabe ta fitar da sakamakon zaben shugabancin kasa na kananan hukumomi 86 daga cikin 308, da aka gudanar a ranakun Lahadi da Litinin.
Sai dai hudu daga cikin ‘yan takarar daga bangaren adawa sun ce ba su amincewa da sakamakon bisa zargin yin magudi.
a tsarin dokar zaben Nijar dai kwanaki biyar aka kayyade domin bayyana kammalallen sakamkon zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisu.
‘Yan takara 14 ne suka fafata da Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou na Jam’iyyar PNDS Tarayya kuma alamu na tabbatar da cewa shi zai lashe zaben tun a zagaye na farko.
CENI ta yi watsi da zargin 'Yan adawar Nijar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu