Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben Nijar

Jam’iyyun adawa a Jamhuriyyar Nijar sun ce ba za su amince da sakamakon farko na zaben shugaban kasa ba inda shugaba Mahamadou Issoufou ke kan gaba a zaben.  

'Yan Nijar na dakun sakamakon zaben shugaban kasa da na 'Yan majalisu
'Yan Nijar na dakun sakamakon zaben shugaban kasa da na 'Yan majalisu ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

‘Yan adawar sun bukaci magoya bayansu su yi watsi da sakamakon zaben.

Mai magana da yawaun ‘Yan adawar Amadou Babacar Cisse ya ce ba zasu amince da sakamakon da hukumar Zaben kasar CENI ta sanar ba.

‘Yan takara 14 ne suka fafata da Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou na Jam’iyyar PNDS Tarayya kuma alamu na tabbatar da cewa shi zai lashe zaben tun a zagaye na farko.

An gudanar da zaben dai cikin kwanciyar hankali amma ‘Yan adawa sun soki hukumar zabe da gazawa musamman na rashin kai kayan zabe a wasu yankunan kasar da dama da suka jefa kuri’a a ranar Litinin.

Babu dai wani cikakken dalili da ‘Yan adawar suka bayar kan yin watsi da sakamakon na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.