Isa ga babban shafi
Nijar

AU ta yaba da halayen ‘Yan Nijar

Kungiyar Tarayyar Afrika ta yaba da halayen ‘Yan Nijar kan yadda suka gudanar da babban zaben kasar cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata hatsaniya ba.

Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou na kada kuri'ar neman wa'adin shugabanci na biyu
Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou na kada kuri'ar neman wa'adin shugabanci na biyu REUTERS
Talla

An gudanar da zaben ne cikin tsauraran matakan tsaro inda ake da ababan hawa masu yawa da ke sintiri domin ganin anyi komi cikin kwanciyar hankali.

Al’ummar Nijar kimanin miliyan bakwai da rabi ke da ‘yancin kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki, a kimanin mazabu dubu ashirin da biyar da ke fadin kasar.

‘Yan takara 15 ne ke fafatawa a zaben, ciki har da shugaban kasa Mahammadou Isoufou da ke neman wa’adi shugabanci na biyu.

Kuma ana zaben ne yayin da guda daga cikin ‘yan takarar kuma tsohon shugaban majalisar kasar Hama Amadou ke tsare a gidan kaso.

Shugaba Issoufou ya kada kuri’arsa tare da iyalan shi a mazaba ta farko da ke birnin Yamai, akan idon wakiliyarmu Koubra illo, kuma ta aiko da rahoto.

01:37

Rahoton Koubra kan Zaben Nijar na 2016

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.