Niger
Kotu a Niger ta Amince ayi Zabe Ba tare da katin shaida ba
Babbar kotun kasar Niger yau asabar ta zartas da hukunci don barin mutane marasa takardun shaida, wato ID Card su jefa kuri'arsu a babban zaben kasar da za'ayi a lahadi.
Wallafawa ranar:
Talla
Gwamnatin Niger ta nemi a bar jama'a su jefa kuria idan basu da takardun shaida, muddin suna da wadanda za su iya gane su cewa 'yan kasa ne da suka cancanci jefa kuria.
‘Yan adawa ne suka soki wannan mataki, amma kuma kotun tsarin mulkin kasar, ta kawar da bukatar ‘yan adawan, kamar dai yadda Kadri Umaru Sanda, mutun na biyu a Hukumar Zabe mai zaman kanta a kasar ya sanar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu