Isa ga babban shafi
Niger

Ana Zaben Shugaban Kasar Nijar Yau

Al’ummar kasar Niger na zaben shugaban kasa yau lahadi, inda ‘yan takara 15 ke fafatawa, ciki har da shugaba mai ci Mahammadu Issoufou dake neman wa'adi na biyu.Majiyoyin samun labarai na cewa babu wani mummunar labari ya zuwa wannan lokaci. 

Wasu daga cikin 'yan takaran shugabancin kasar Nijar
Wasu daga cikin 'yan takaran shugabancin kasar Nijar
Talla

Har ila yau za’a gudanar da zabukan wakilan majalisar Dokokin kasar a yau.

Bayanai na nuna an dauki tsauraran matakan tsaro inda ake da ababan hawa masu yawa dake sintiri domin ganin anyi komi cikin kwanciyar hankali.

Jimillan mutane kusan miliyan takwas ne ake saran zasu jefa kuri'arsu a yau, kuma ana ganin kasa da kwanaki biyar ne za’a bayyana sakamakon wannan zabe na yau.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.