Mayakan Boko Haram sun mika kansu a Nijar
Mayakan Boko Haram 31 sun mika kansu ga hukumomin Jamhuriyar Nijar kamar yadda ministan cikin gidan kasar, Bazoum Mohamed ya sanar.
Wallafawa ranar:
Ministan ya ce, mayakan sun kuma mika makamansu a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin kasar, kuma a karon farko kenan da mayakan suka yi haka a kasar.
Majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, a halin yanzu an killace mayakan a wuri guda don ba su horon da zai sauya tunaninsu kafin daga bisani su koma ga iyalansu.
Tun a cikin watan Fabairun shekarar 2015 ne, kungiyar Boko Haram ta tsananta kaddamar da munanen hare-hare a Nijar, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Tuni dai Kasashen Nijar da Najeriya da Kamaru da Chadi suka kaddamar da shirin kakkabe kungiyar Boko Haram da ta salwantar da rayukan al’umma da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu