Isa ga babban shafi
Nijar

Mazauna Diffa sun koka bisa fuskantar matsi daga jami'an tsaro

Mazauna yankin Diffa a jamhuriyar Nijar sun bukaci hukumomi su dauki matakai, dangane da yadda jami’an tsaro ke amfani da dokar ta baci da aka kafa a yankin saboda ayyukan Boko Haram, wajen cin zarafin jama’a.

Wani sashi na yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, da masu gudun hijira ke zama
Wani sashi na yankin Diffa da ke Jamhuriyar Nijar, da masu gudun hijira ke zama
Talla

Alhaji Yacouba Danmaradi, wanda ya ziyarci yankin a ‘yan kwanakin nan, ya ce jami’an tsaron na takurawa jama’a matuka.

A hirarsa da sashin Hausa da RFI Alhaji Yacouba ya ce jami’an tsaron na wuce gona da iri wajen tsanantawa al’ummar da ke zaune a yankin.

Zalika ya kara da cewa hatta kekunan da yara ‘yan makaranta ke amfani da su wajen zuwa makaranta, jami’an tsaron na tilasta sai an biya harajin amfani da su a yankin.
Alhaji Yacouba ya kuma ce wata sabuwar matsalar da mazauna yankin na Diffa ke fuskanta shi ne karbar kudade da jami’an tsaron da ke wajen ke yi daga hannun jama’a bisa katin shaidar zama dan kasa, muddin suka tare su a shingayen binciken ababen hawa.

A karshe yayi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar sun sauke nauyin da ay rataya a wuyansu isa tsarin da doka ta tanada tare da sassautawa al’umma.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.