Mayakan jihadi sun kai hari a gidan yarin Nijar
Rahotanni daga birnin jamhuriyar Nijar na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a sanyin safiyar yau a kan gidan yarin Koutou Kale mai tazarar kilomita 50 a yammacin birnin Yamai.
Wallafawa ranar:
Bayanai na nuni da cewa akwai alamar maharan masu da’awar jihadi ne kuma suna kokarin ceto magoya bayansu da ke tsare a gidan yarin.
Wasu bayanan sun ce, an tura karin jami’an tsaro domin kai dauki ga jami’an da ke kula da gidan yarin, wanda shi ne mafi tsaro a duk fadin kasar ta Nijar.
Mafi yawa daga cikin wadanda ake zargi da ayyukan ta’addanci da aka kama a iyakar kasar ta Nijar da Mali da kuma ‘yan Boko Haram da aka kama a yankin Diffa, ana tsare da su ne a wannan gidan yari na Koutou Kale.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu