Isa ga babban shafi
Nijar

Mayakan Boko Haram sun sake kai hari a garin Tumour

'Yan kungiyar Boko haram sun sake kaiwa mutanen garin Tumour hari, inda aka bayyana cewa Sojojin Nijar dake sintiri a harabar garin na Tumour sun gwabza fada da mayakan na Boko Haram. 

Shugaban sashin kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban sashin kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Wani mazaunin garin na Tumour da ya nemi a sakaye sunan sa, ya ce a lokacin da mayakan na Boko Haram suka sake kutsawa garin na Tumour, sun kama Filani guda uku inda suka umurce su, da su nuna musu gawarwarkin mayakansu da aka kashe.

Sai dai mayakan basu samu nasarar daukar gawarwakin ‘yan uwansu ba jami’an soji suka yi musu dirar mikiya, aka cigaba da musayar wuta kafin daga bisani sojojin su samu nasarar korar mayakan.

Mazaunin garin ya ce yawan ‘yan Boko Haram din da suka kutsa garin, sun kai 100 akan dawakai da rakuma.

Game da halin da ake ciki kuwa a garin na Tumour, mazaunin ya ce mutane suna zaune cikin gidajensu, in banda ‘yan sintiri na sa kai da ke zagaya garin dauke da kwari da baka, sai kuma sauran jami’an tsaro da ke sintiri.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.