Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu cafke Muhammadu Buhari- Boko Haram

Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon hoton bidiyo,in da ta sanar da shirinta na cafke shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan ta bayyana shi a matsayin kafiri.

Boko Haram ta yi barazanar cafke shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Boko Haram ta yi barazanar cafke shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya HO / BOKO HARAM AFP / AFP
Talla

Bidiyon wanda ake zaton an dauka ne a wani boyayyen wuri a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya, ya nuna mayakan na gudanar da sallar idi a ranar litinin.

Kungiyar ta ce, da yardan Allah za ta kama shugaba Buhari da hannunta kuma a karkashin jagorancin Abubakar Shekau.

Kazali kungiyar ta jaddada cewa, har yanzu tana da karfi duk da rahotannin da ke cewa, ta rasa wuraren da ta ke da iko da su, yayin da sojojin kasar ke ci gaba da ragargazar ta.

Sai dai a wannan karon, jagoran na kungiyar, Abubakar Shekau bai bayyana a cikin bidiyon ba wanda aka yada a cikin harshen hausa, in da mataimakinsa ya wakilce shi wajen isar da sakon.

Kimanin wata guda da ya wuce, kungiyar fitar da wani bidiyo, in da ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta yi musayar fursunonita da ‘yan matan Chibok da ta sace, matakin da gwamnatin ta ce, za ta yi nazari a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.