Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci tsaurara tsaro a arewa maso gabshin Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane da dama da rikicin Boko Haram ya dai-daita arewa maso gabashin Najeriya suna koma gidajensu, sakamakon nasarar da sojojin kasar ke yi kan mayakan na Boko Haram.  

Wasu yara da ke sansanin 'yan gudun hijira a garin Maiduguri
Wasu yara da ke sansanin 'yan gudun hijira a garin Maiduguri OCHA/Jaspreet Kindra
Talla

Sai dai kuma Majalisar Dinkin Duniyar ta yi gargadin yiwuwar fuskantar hare-hare jefi-jefi, daga kungiyar ta Boko Haram, da mutanen da ke komawa kauyuka a arewa maso gabashin Najeriyar ka’iya fuskanta, hadi da rashin ababen more rayuwa.

A cewar mai Magana da sashin kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinki Duniya Leo Dobbs akwai bukatar ganin an gaggauta sake ginin yankunan da rikicin ya rusa, tare da wadata mutane da abinci domin kaucewa yunwa a yankin.

A baya Majalisar Dinkin Duniyar ta yi gargadin cewa kimanin yara dubu dari biyar ke fuskantar hadarin kamuwa da yunwa a yankin tafkin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.