Isa ga babban shafi

Mayakan sa kai 11 ne suka mutu bayan da motarsu ta taka nakiya a Najeriya

Wasu mayakan sa kai guda 11 da ke yaki tare da sojojin Najeriya masu yakar yan ta’adda suka mutu a yau Asabar a yankin arewa maso gabashin Najeriya a lokacin da motarsu ta taka nakiya a kusa da kan iyaka da kasar Kamaru.

Wasu daga cikin hanyoyin shiga Maiduguri a Najeriya
Wasu daga cikin hanyoyin shiga Maiduguri a Najeriya BOKO HARAM/AFP/File
Talla

Majiyar ta bayyana cewa mayakan jihadi dai na kara yin amfani da nakiyoyi a kan tituna a wannan yaki na sunkuru da suke yi da dakarun Najeriya wajen kai hare-hare kan fararen hula tun bayan da aka fatattaki su daga yankunan da suke iko da su a shekarun farko na tada kayar bayan da suka shafe shekaru sama da 15 ana yi.

Mayakan sa kai a lokacin faruwar lamarin,na rakiyar ayarin fararen hula ne da suka taso daga garin Gamboru na jihar Borno, zuwa Maiduguri babban birnin yankin, a lokacin da motarsu ta taka nakiya da ake zargin mayakan boko Haram ne suka sanya a kauyen Damno, kamar yadda majiyoyin suka bayyana. .

Wasu jami'an tsaron Najeriya a wani wuri da aka samu fashewa a Yola dake jihar Adamawa. 25/02/2016
Wasu jami'an tsaron Najeriya a wani wuri da aka samu fashewa a Yola dake jihar Adamawa. 25/02/2016 ASSOCIATED PRESS - AP Photo

"Tayoyin bayan motar da ke dauke da ‘yan sa kai 13 yan lokuta da wuce wani katon rami da aka binne wata nakiya a cikinsa wadda ta fashe," in ji Shehu Mada, shugaban mayakan sa kai a Gamboru. "Mutane 11 da ke cikin motar sun mutu, biyu kuma sun jikkata."

An fitar da wadanda abin ya rutsa da su ne daga ragowar motar kuma aka mayar da su Gamboru domin yi musu jana’iza kamar yadda wani dan banga Usman Hamza ya bayyana.

Gadar da gwamnatin Kamaru ta sake ginawa bayan Boko Haram ta rusa ta a 2015.
Gadar da gwamnatin Kamaru ta sake ginawa bayan Boko Haram ta rusa ta a 2015. © Premiumtimes

Hare-haren yan bindiga sannu a hankali ya ragu matuka a Najeriya a tsawon lokacin da sojoji ke kai wa mayakan jihadi farmaki.

Hanyar da ta hada Gamboru zuwa Maiduguri hanya ce mai nisan kilomita 140 don kasuwanci ga yankin da dangantakarsa da makwabciyarta Kamaru.

Wani sojan Kamaru a wani shingen tsaro da ke kan gadar Elbeid, wadda ta raba arewacin Kamaru da jihar Borno da ke Najeriya a kusa da kauyen Fotokol na kasar Kamaru.
Wani sojan Kamaru a wani shingen tsaro da ke kan gadar Elbeid, wadda ta raba arewacin Kamaru da jihar Borno da ke Najeriya a kusa da kauyen Fotokol na kasar Kamaru. ASSOCIATED PRESS - Edwin Kindzeka Moki

An sake bude hanyar ne a watan Yulin 2016, bayan da sojoji suka rufe tsawon shekaru biyu saboda hare-haren da mayaka masu ikirarin jihadi ke kaiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.