Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kai kazamin hari Bilbis dake Jihar Zamfara

Najeriya – ‘Yan ta’adda a Najeriya sun kai mummunan hari a garin Bilbis dake Jihar Zamfara inda suka kashe mutane kusan 20 da suka kunshi maza da mata da kuma kananan yara.

Gwamna Dauda Lawal
Gwamna Dauda Lawal © Daily Trust
Talla

Rahotanni sun ce wadannan ‘yan ta’adda sun kai harin ne jiya alhamis inda suka kwashe sama da sa’oi 2 suna aika aika tare da jikkata mutane da dama a garin, kuma yanzu haka wasu daga cikin su na asibiti inda suke karbar magani.

Shaidun gani da ido sun bayyanawa Jaridar Premium Times cewar, ‘yan ta’addan sun kai harin ne a kan babura, inda suka toshe duk hanyoyin shiga garin, tare da kai hare hare a kan jama’a.

Bayanai sun ce, wasu daga cikin wadanda aka kashe na daga cikin wadanda suka nemi gudu domin tsira da rayukan su, yayin da wasu kuma har cikin gidajen su aka hallaka su.

Rahotanni sun ce a safiyar yau juma’a aka yi janaizar wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan kazamin harin.

Garin Bilbis da kuma karamar hukumar Tsafe sun gamu da munanan hare haren ‘yan ta’addan da suka hana zaman lafiya a jihar Zamfara a yan watannin da suka gabata.

Mutanen yankin sun dade suna gabatar da bukatar girke musu karin jami’an tsaro domin tinkarar wadannan bata gari, amma har yanzu babu cikkaken zaman lafiyar da aka gani a garuruwan dake karamar hukumar.

Garuruwan Tsafe da Zurmi da Maradun da Anka da Bungudu a Jihar Zamfara da makotanta na Katsina da Kaduna da Neja da kuma Sokoto sun zama dandalin zubar da jini daga wadannan ‘yan ta’addan da basa mutunta rayukar jama’a.

Yanzu haka garuruwa da dama a wadannan jihohi sun zama kango saboda yadda mutanen dake cikin su suka fice domin komawa birane idan suke zaton tsira da rayukansu.

Haka zalika, wasu dake kusa da iyakokin Jamhuriyar Nijar sun tsallaka iyaka domin samun mafaka daga wadannan ‘yan ta’adda.

Ko a farkon makon nan, hukumomin Jamhuriyar Nijar sun kama daya daga cikin fitattun ‘yan ta’addan da ake kira Kachalla wanda ya yi kaurin suna wajen kai munanan hare hare a kan mutanen dake jihar Zamfara da Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.