Isa ga babban shafi

Ƴan bindida sun kashe mutane 25 a wasu ƙauyukan arewa maso yammacin Najeriya

A Najeriya ‘yan bindiga sun kashe mutane 25 a wani samame da suka kai wasu ƙauyuka 4 a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar, martani da suka yi ga hare-haren da sojojin ƙasar suka kai maɓuyarsu, kamar yadda majiyoyi a yankin suka bayyana.

'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya. © Leadership
Talla

Ƴan bindigar  sun kutsa kauyukan Unguwar Sarki, Gangara, Tadi da Kore a gundumar Sabuwa ta jihar Katsina a daren Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, a cewar kwamishinan tsaron jihar, Nasiru Babangida.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke ɗanɗana kuɗarsu a hannun ‘yan bindiga da ke cin karensu ba babbaƙa a arewa maso yammacin ƙasar, inda suke kisa tare da satar mutane don karɓar kuɗin fansa.

Mazauna ƙauyukan da dama ne suka samu rauni sakamakon waɗannan hare-hare, a yayin da ƴan bindigar suka yi awon gaba da da dama daga cikin su.

Rahotanni sun ce akasarin waɗanda suka mutu ƴan sa-kai ne da ke bai wa al’ummominsu kariya daga ayyukan ƴan bindiga masu  kisa da satar mutane.

Yawancin al’ummomi a arewa maso yammacin Najeriya sun kafa ƙungiyoyin sa-kai don yaki da ƴan bindiga da suka hana su sakat, sakamakon rashin wadatuwar jami’an tsaro.

Masana harkar tsaro dai sun yi ittifakin cewa waɗannan ƴan bindiga ba su da wata aƙida, kuma su na samun ƙwarin gwiwa ne kawai daga kuɗin da ake samu a satar mutane, sai dai sun bayyana damuwa a kan yadda  ake ci gaba da samun haɗaka tsakanin ƴan bindiga da ƴan ta’adda masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.