Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar Dutsin-Ma da ke Katsina

A yayin da ake tababa kan bayanan da ke cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’ar tarayyar Najeriya da ke garin Gusau a Zamfara, rahotanni daga jihar Katsina a baya bayan nan sun ce ‘yan ta’addan sun kai hari kan jami’ar tarayya da ke garin Dutsin-Ma.

Alamar 'Yan bindiga masu da suka addabi 'yan Najeriya.
Alamar 'Yan bindiga masu da suka addabi 'yan Najeriya. © Daily Trust
Talla

Bayanai sun ce lamarin ya auku ne da misalin karfe 2 na dare, gabanin asubahin wannan Laraba, inda maharan suka sace dalibai 5 bayan da suka afka wa rukunin dakunansu.

Jaridar Daily Trust da ake wallafa ta a Najeriya ta ruwaito cewa, daliban da aka sace sun fito ne daga jihohin Nasarawa da kuma Kano.

Wasu dalibai a jami’ar ta Dutsin-Ma sun ce kafin harin ‘yan bindigar, hukumar makarantar ta su, ta yi kokarin dakile yiwuwar aukuwar mummunan lamarin ta hanyar ba su umarnin kasancewa a dakunansu da zarar an kai karfe 10 na dare, sakamakon rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’ar tarayya da ke garin Gusau.

A halin da ake ciki, rundunar ‘Yan Sandan Katsina ta hannun kakakinta ASP Sadiq Aliyu Abubakar, ta sanar da cafke wasu mutane da ba ta bayyana adadinsu ba, bisa zarginsu da hannu a harin da ‘yan bindigar suka kai, cikinsu kuwa har da wani da ake tuhuma da taimaka wa ‘yan ta’addan bayanai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.