Isa ga babban shafi
KWALLON KAFA

Yau ake cika shekaru 12 da rasuwar Rashidi Yekini

Najeriya – Yau ake cika shekaru 12 da rasuwar Rashidi Yekini, daya daga cikin gwarzon 'yan wasan Najeriya da suka taka rawa sosai wajen daga sunan kasar a duniya.

Tsohon dan wasan gaba na tawagar Najeriya Rashidi Yekini
Tsohon dan wasan gaba na tawagar Najeriya Rashidi Yekini © Premium Times
Talla

Yekini ya rasu ne ranar 4 ga watan Mayun shekarar 2012 yana da shekaru 48  a duniya, bayan ya yi ritaya daga buga wasa.

An dai haife shi ne a garin Kaduna a ranar 23 ga watan  Oktobar shekarar 1963, kuma a nan ya fara wasan kwallon kafar da ta kai shi bugawa kungiyoyi 12 a duniya.

Daga cikin kungiyoyin da ya yiwa wasa akwai kungiyar UNTL dake Kaduna tsakanin shekarar 1981 zuwa 1982, sai Shooting Stars ta Ibadan, tsakanin shekarar 1982 zuwa 1984 sannan kungiyar Abiola Babes dake Abeokuta, tsakanin shekarar 1984 zuwa 1987.

Yekini ne na farko daga gefen hagu cikin wadanda suke tsugune a cikin tawagar da ta wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniyar shekarar 1994
Yekini ne na farko daga gefen hagu cikin wadanda suke tsugune a cikin tawagar da ta wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniyar shekarar 1994 © The Guardian

Daga nan ne Rashidi ya koma kungiyar Africa Sports dake Abidjan inda ya yiwa kungiyar wasa tsakanin shekarar 1987 zuwa 1990, abinda ya bashi damar tafiya nahiyar Turai domin zama daya daga cikin fitattun 'yan wasan Najeriya.

Bayan ya yi fice a Afirca Sports, Yekini ya koma kungiyar Victoria Setubal dake Portugal inda ya yi mata wasa na shekaru 4 tsakanin shekarar 1990 - 1994, kafin ya koma Olympiakos wadda ya yiwa wasa tsakanin shekarar 1994 - 1995, sai kuma Sportin Gijon tsakanin shekarar 1995 - 1996.

A shekarar 1997 Yekini ya sake komawa Victoria Setubal, kafin daga bisani ya koma FC Zurich tsakanin shekarar 1997 - 1998, sai kuma Bizerte tsakanin shekarar 1998 - 1999, sannan kungiyar Al Shebaab ta Saudi Arabia a shekarar 1999.

A shekarar 1999 Yekini ya sake komawa Africa Sports har zuwa shekarar 2002, kafin daga bisani ya koma Julius Berger ta Najeriya tsakanin shekara ta 2002 zuwa 2003, sai kuma Gateway ta Abeokuta a shekarar 2005 kafin ya yi ritaya.

Alkaluma sun nuna cewar ya buga wasanni 253 a wadannan kungiyoyi, tare da jefa kwallaye 164.

A bangaren yiwa kasa wasanni kuma, Yekini ya buga wasanni 62 wa Najeriya tare da jefa kwallaye 37.

Rashidi Yekini
Rashidi Yekini © Premium Times

Tauraron 'dan wasan na daga cikin wadanda suka lashe gasar cin kofin Afirka wa Najeriya a shekarar 1994 da kuma taimakawa kasar zuwa gasar cin kofin duniya na farko a Amurka a cikin wannan shekarar, inda ya zama 'dan wasa na farko da y afara jefawa Najeriya kwallo a raga.

Daga cikin lambobin girmamawa da ya samu, akwai lambar zakaran 'dan wasan Afirka da yafi kowa fice ta shekarar 1993 da kyautar zama 'dan wasan da yafi zirara kwallo a gasar cin kofin Afirka na shekarar 1992 da 1994.

'Yan Najeriya da dama na girmama marigayin saboda saukin kansa da kuma irin gudumawar da ya bayar wajen daga darajar Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.