Isa ga babban shafi

Yau ake cika shekaru 14 da rasuwar tsohon shugaban Najeriya Umaru Musa 'Yar Adua

Najeriya – Yau aka cika shekaru 14 da rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Malam Umaru Musa 'Yar Adua, daya daga cikin shugabannin da 'yan Najeriya ke matukar girmamawa bayan kwashe kusan shekaru 3 a karagar mulki.

Tsohon shugaban Najeriya marigayi Umaru Musa Yar'Adua
Tsohon shugaban Najeriya marigayi Umaru Musa Yar'Adua REUTERS/Finbarr O'Reilly
Talla

An dai haifi marigayin ne a ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951, a garin Katsina, kuma mahaifinsa tsohon minista ne a jamhuriya ta farko, yayin da wansa Janar Shehu Musa 'Yar Adua ya zama daya daga cikin jiga jigan gwamnatin mulkin sojin Najeriya tun daga lokacin Janar Yakubu Gowon har zuwa lokacin da Janar Olusegun Obasanjo ya mika mulki ga gwamnatin shugaba Shehu Usman Aliyu Shagari a shekarar 1979.

Malam Umaru Musa 'Yar Adua yayi malamin makaranta kafin ya kutsa kai cikin harkokin siyasa, abinda ya kai shi samun nasarar zama gwamnan Katsina tsakanin shekarar 1999 zuwa shekarar 2007.

Lokacin da ak adauki gawar Malam Umaru Musa Yar Adua daga Abuja zuwa Katsina
Lokacin da ak adauki gawar Malam Umaru Musa Yar Adua daga Abuja zuwa Katsina © Reuters

Lokacin da shugaba Obasanjo ya kawo karshen wa'adin mulkinsa a shekarar 2007, ya goyi bayan Umar Musa Yar Adua daga cikin tarin 'yan takarar da suka nemi tsayawa zabe a jam'iyyar su ta PDP, abinda ya kai shi ga samu nasarar kayar da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cikin shekaru kusan 3 da ya yi yana jagorancin Najeriya, Malam Umaru Musa Yar Adua ya samu karbuwa sosai a tsakanin talakawan kasar saboda kyawawan manufofinsa da ya gabatar domin inganta rayuwar su tare da rage farashin man da ya gada daga gwamnatin Obasanjo.

Wadannan manufofi sun hada da inganta bunkasa bangaren ilimi da kula da lafiya da samar da kayan more rayuwa da inganta samar da wutar lantarki da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin Neja Delta.

A lokacin sa ne gwamnatin Najeriya ta sasanta rikicin Neja Delta wajen tabbatar da zaman lafiya da inganta samar da man fetur tare da horar da matasan yankin a kan sana'oi daban daban a ciki da wajen Najeriya.

Lokacin sallar gawar Malam Umaru Musa Yar Adua
Lokacin sallar gawar Malam Umaru Musa Yar Adua REUTERS/S. Maikatanga

Tsohon shugaban ya amince da kura kuran da ake samu wajen harkar zabe, inda ya nada kwamiti na musamman a karkashin tsohon mai shari'a Muhammad Lawal Uwais domin bada shawarar yadda za'a inganta wannan bangare, wanda ya kaiga aiwatar da sauye sauye da kuma nada Farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban hukumar zabe na kasa.

'Yar Adua ya kuma soke sayar da matatun man kasar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi tare da tinkarar matsalar karancin man fetur wanda ya gada daga gwamnatin da ta gabace shi.

Shugaban wanda ya kaddamar da aikin janyo teku daga kudancin Najeriya zuwa arewacin kasar domin ragewa 'yan kasuwa wahalar da suke sha wajen daukar kayan su a tashoshin jiragen ruwan dake kudancin kasar ya yi ta fama da rashin lafiyar da ta hana shi gudanar da ayyukansa kamar yadda suka kamata, abinda ya kai ga rasuwarsa a rana mai kamar ta yau ta 5 ga watan Mayun shekarar 2010.

Shugaba Olusegun Obasanjo, marigayi Umar Musa Yar Aduwa da Goodluck Jonathan.
Shugaba Olusegun Obasanjo, marigayi Umar Musa Yar Aduwa da Goodluck Jonathan. Sahara Reporters

Daya daga cikin ministocinsa, Sanata Ikra Aliyu Bilbis, ya bayyana tsohon shugaban a matsayin jagora na gari, wanda kan zauna da ministocinsa daya bayan daya, yana tattaunawa da su a kan manufofin gwamnatinsa da kuma irin rawar da yake so su taka a kan aikin da ya ba su domin ci gaban kasa.

Tsohon mataimakinsa kuma shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana Yar Adua a matsayi jagora na gari, mai bin doka da oda a cikin duk wasu matakan da yake dauka wajen shugabancin kasa.

"Akwai abubuwa da dama da za a iya tuna tsohon shugaban dasu," in ji Sanata Ikra Bilbis.

04:18

Jawabin Sanata Ikra Bilbis kan irin gudun mowar da tsohon shugaban ya bayar

'Yan Najeriya da dama na kallon tsohon shugaban a matsayin mai gaskiya da amana da kuma iya shugabanci tare da kishin kasa lokacin da ya yi mulkinsa, yayin da irin salon mulkin sa da kuma sanya ido a kan jami'ansa ya banbanta da shugabannin da suka biyo bayan sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.