Isa ga babban shafi

Ba zan sake tsayawa takarar zabe ba - Gwamnan Nasarawa

Najeriya – Gwamnan Jihar Nasarawa dake Najeriya, Abdullahi Sule yace ba zai sake tsayawa takarar zabe ba, muddin ya kammala wa'adin mulkinsa na shekaru 8.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa kenan.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa kenan. © dailytrust
Talla

Sule wanda yake tsokaci bayan nasarar da ya samu a kotun koli wadda ta tabbatar da zaben da aka masa bara, yace aniyarsa itace ta zama gwamna saboda shirin da yake da shi ga mutanen sa, kuma da zaran ya kammala wa'adin sa, zai kawo karshen shiga takarar zabe.

Gwamnan yace baya tunanin sake neman takarar zama Sanata ko kuma shugaban kasa ko kuma shugaban jam'iyyar, domin basa cikin abinda yake sha'awa.

Abdullahi Sule ya zama gwamnan jihar Nasarawa ne sakamakon zaben shekarar 2019, yayin da ya nemi wa'adi na 2 kuma ya yi nasara a shekarar da ta gabata, amma jam'iyyar PDP tayi zargin tafka kura kurai a zaben, abinda ya sa kotun sauraron shari'ar zabe ta soke nasarar.

Gwamnan ya samu nasara a kotun daukaka kara da kuma kotun koli, abinda ya kawo karshen kalubalantar nasarar da ya samu. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.