Isa ga babban shafi

Babu tantama zamu sake duba sabbin masarautun Kano - Kwankwaso

Najeriya – Tsohon Gwamnan Jihar Kano dake Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso yace babu tantama zasu sake duba batun masarautar Kano wadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta karkasa zuwa masarautu guda 5.

Rabi'u Musa Kwankwaso
Rabi'u Musa Kwankwaso © Premiumtimes
Talla

Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, Kwankwaso yace ya zuwa wannan lokaci babu wanda ya zauna da shi domin tattauna batun, amma kuma duk da haka yace zasu duba lamarin nan gaba domin sanin matakan da ya dace a dauka da suka hada da barín sabbin masarautun ko rusa su, ko kuma yi musu gyaran fuska.

Kwankwaso ya bayyana matakan da tsohuwar gwamnati ta dauka dangane da masarautun a matsayin gadar zare, wanda aka yi shi ba tare da manufa mai kyau ba.

Tsoffin gwamnonin Kano Abdullahi Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso
Tsoffin gwamnonin Kano Abdullahi Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso © RFI Hausa

Tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro sabbin masarautu a jihar bayan ya warware nadin tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na 2.

Batun sake duba matsayin sabbin masarautun na daga cikin abinda zababben gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya yi yakin neman zabe da shi, sai dai wasu mutane na bukatar taka tsantsan a kan lamarin wanda suka ce na iya haifar da tashin hankali a jihar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.