‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa a kan yadda kotuna ke karbe hurumin da kundin tsarin mulki ya bai wa Hukumar zabe na bayyana wadanda suka samu nasarar zabubbukan da jama’a suka yi, wajen bayyana wasu daban a matsayin halartattun wadanda suka yi nasara.
Wannan ya biyo bayan yadda kotunan suka sauya sunayen wadanda hukumar zabe ta sanar sun samu nasara a zabbubukan gwamnoni da kuma ‘yan majalisun kasar.
Ko a wannan mako, kotuna sun soke zabubbukan gwamnonin Zamfara da Kano, yayin suka tabbatar da na jihohin Lagos da Bauchi.
Dangane da wannan korafi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hajiya Naja’atu Muhammad, ‘yar siyasa, kuma mai sharhi akan harkokin Najeriya.
Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu