Isa ga babban shafi

Gwamnatin Kano ta gano yadda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta dauki daliban sakandire aiki

Gwamnatin Kano ta gano yadda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje, ta dauki ma’aikatan da basu cancanta ba, ciki har da wadanda suke aji uku a makarantun sakandire.

Ganduje ya jagoranci jihar Kano, karkaashin jam'iyyar APC, har tsawon shekaru takwas.
Ganduje ya jagoranci jihar Kano, karkaashin jam'iyyar APC, har tsawon shekaru takwas. © DailyTrsut
Talla

Jaridar Dailytrust ta ruwaito cewa, tun bayan da gwamnatin jihar karkashin Abba Kabir ta karbi mulki, ta dakatar da wasu ma’aikata da ta ce an dauka ba bias tsarin doka ba.

Hakan ta sanya aka kafa kwamitin da zai bibiyi wannan al’amari, domin tantancee ma’aikatan da suka dace a bari.

Da yake zantawa da manema labarai, sakataren gwamnatin jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi, y ace kwamitin ya gano cewa gwamnatin baya, tay dauki ma’aikata da yawa, amma kuma ta kauce hanya.

Ya kara da cewa, kwamitin ne ya bayar da shawarar a sallami mutum 3,000 da aka gano basu cancanta ba.

Kwamitin tantance ma’aikatan ya ce, ma’aikatan da aka dauka tuni aka tura su hukumomi da ma’aikatun gwamnati a wancan lokaci, amma yanzu an dawo da wasu daga cikinsu da aka gama tantancewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.