Isa ga babban shafi

Babu shakka za mu kalubalanci wannan hukunci - Abba Kabir Yusuf

‘Yan sa’o’i da hukunchin kotu na soke zaben sa a matsayin gwamnan jihar Kano a Najeriya, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce ba shakka zai kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf © Abba Kabir Yusuf
Talla

A cikin wani jawabi da ya gabatar wa Kanawa cikin daren Laraba, Gwamna Abba Kabir ya ce ko kadan hukuncin ba zai sare masa gwiwa ba. 

Da maraicen Laraban ne dai kotun sauraren kararrakin zabe ta bayyana dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben jihar da rinjayen kuri’un da aka kada, hukuncin da ke kawar da nasarar Injiniya Abba Kabir Yusuf da tuni ya fara jan ragamar jihar. 

Tuni dai wannan hukunci ya sanya zullumi kan yiwuwar samun tashe-tashn hankula a sassan jihar, batun da masu sharhi kan harkokin siyasa ke cewa akwai bukatar kwantar da hankula tare da kaucewa rikici. 

Ku latsa alamar sauti domin sauraran Abba Gida-Gida

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.