Isa ga babban shafi

Za mu kashe alkalan da suka soke zaben gwamnan Kano - Kwamishina

Kwamishinan filaye na jihar Kano dake arewacin Najeriya, Dr. Adamu Aliyu Kibiya, ya yi barazanar kisa ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a jihar muddun suka soke nasarar gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf a zaman shari’ar da ke tafe.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf © Abba Kabir Yusuf
Talla

Mista Aliyu ya kuma yi alkawarin tayar da hankulan al’ummar jihar Kano, ta yadda mazauna makwabtan ta jihohin Kaduna da Zamfara sai sun fi su jin dadi.

Sanin kowa ne wadannan jihohin biyu dai na fama da hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane, sun kwashe shekaru da dama suna kashe bayin Allah babu gaira babu dalili.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne wannan Alhamis yayin wani jawabi da ya yi wa magoya bayan jam’iyyar NNPP a jihar gabanin zaman kotun sauraran kararrakin zabe da ke tafe a jihar.

“Ina aike da wannan sako ga alkalan kotu, duk wani alkali da ya bari a yi amfani da shi ya karbi cin hanci ya yanke hukuncin da bai dace ba, muna so mu fada masa ya zabi tsakanin rayuwarsa da kudin cin hancin da ya karba”.

Ya na cewa akwai yuwuwar an baiwa alkalan kotun cin hanci don baiwa APC nasara, matakin da ya ce muddun suka aikata haka to sun sayar da rayukansu kenan.

Nasiru Gawuna na APC

Nasiru Gawuna ne ke kalubalantar zaben gwamnan jihar, Abba Yusuf a gaban kotun. Kuma har yanzu kotun ba ta tsayar da ranar da za ta yanke hukunci kan karar ba.

Magoya bayan jam’iyyar NNPP sun yi gangami tare da zaman addu’o’in samun sakamako mai kyau ga jam’iyyar su a kotun sauraron kararrakin zabe.

Daga bisani dukkan bangarorin jam’iyyun na NNPP da APC suka wallafa faifan bidiyo na kwamishinan da ke yin barazana a shafukan sada zumunta.

Taron addu'o'i

An gudanar da taron muzaharar da addu’o’in a wurare shida da suka hada da titin Katsina da titin Gwarzo da titin Madobi/Sharada da titin Zariya da titin Maiduguri da kuma titin Hadejia.

Taron ya samu halartar sakataren gwamnatin jihar Kano, Baffa Bichi da tsohon mataimakin gwamnan jihar Hafiz Abubakar da kuma manyan ‘yan majalisar zartarwa na jihar da mashawarta na musamman da mataimaka ga gwamnan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.