An kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a Kano
Rundunar ‘yan sanda ta kafa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Kano, matakin da ta dauka, sa’o’i bayan da kotun sauraron kararrakin zaben jihar ta yanke hukuncin kwace kujerar Gwamna daga Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ta kuma mika ta ga Nasiru Yusuf Gawuna na APC.
Wallafawa ranar:
Ana dai kyautata zaton cewar an dauki matakin dokar hana fitar ne domin dakile duk wani yunkuri na yiwuwar tayar da zaune tsaye a sassan jihar ta Kano saboda hukuncin kotun.
Cikin sanarwar da ya rattaba wa hannu da kansa, Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, Muhammad Usaini Gumel, ya bayyana baza jami’an tsaro zuwa sassan jihar domin tabbatar da aikin dokar hana fitar.
Bayanai sun ce tuni mutane suka kauracewa ci gaba da gudanar da hada-hada a titunan birnin na Kano, yayin da a kafafen sada zumunta jama’a ke fadin albarkacin bakinsu kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben na mika wa Nasiru Yusuf Gawuna kujerar gwamnan jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu