Isa ga babban shafi

Zaben Najeriya: 'Yan sanda sun cafke Ado Doguwa a Kano

‘Yan sanda sun kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane tare da kona sakatariyar jam’iyyar NNPP a yayin zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Alhassan Ado Doguwa kenan
Alhassan Ado Doguwa kenan © Nigerian House of Rep
Talla

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa akalla mutane uku ne suka mutu a lokacin da aka kona sakatariyar yakin neman zaben jam’iyyar NNPP da ke Tudunwada.

Mutane biyu ne suka kone kurmus a rikicin da ya barke yayin tattara sakamakon zaben majalisar wakilai ta Doguwa/Tudunwada wanda a karshe aka bayyana Doguwa ne ya lashe zaben.

Wata majiya mai tushe daga rundunar ‘yan sandan ta shaida wa Dailytrust cewa an cafke Doguwa ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja.

Majiyar ta ce rahoton da hukumar ‘yan sanda ta fitar a Tudunwada ya bayyana cewa Doguwa da kansa ya jagoranci ‘yan bangar siyasa suka kona sakatariyar NNPP inda akalla mutane biyu suka kone kurmus.

“Ya kuma yi amfani da bindigar dogarinsa tare da harbin kan mai ‘uwa dawabi. Don haka mun kama shi da laifin kisa da kona wadanda ba su ji ba basu gani ba,” in ji sanarwar.

"A halin yanzu yana amssa tambayoyi a sashen binciken manyan laifuka na jihar Kanoi."

Tun da farko, Doguwa a wata zantawa da manema labarai ya musanta zargin da ake masa, ya kuma ce ya samu labarin cewa ‘yan sanda na neman sa amma bai samu wata gayyata a hukumance ba.

Ya kuma musanta zargin cewa ya harbe wasu mutane da dama a rikicin da ya barke, yana mai cewa shi ba shi da bindiga haka nan bai san harbin bindiga ba.

“Ban taba rike bindiga ba. Ban ma san yadda ake rike bindiga ba. Haka kuma ban taba rike wani makami ba a duk lokacin zaben,” inji Ado Doguwa.

Sai dai ya ce rikicin ya faro ne lokacin da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka zo da nufin kona ofishin INEC kuma magoya bayan APC suka fatattake su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.