Isa ga babban shafi

Najeriya ta yi watsi da zargin shirin girke sojojin Faransa da Amurka a kasar

Najeriya – Gwamnatin Najeriya tayi watsi da rade radin cewar tana fuskantar matsin lamba daga kasashen Amurka da Faransa domin basu damar kafa sansanin sojin su domin yaki da ta’addanci.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, bayan karbar bakuncin Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a Abuja.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, bayan karbar bakuncin Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a Abuja. AP - ANDREW CABALLERO-REYNOLDS
Talla

Ministan yada labaran kasar Mohammed Idris ya bayyana haka kwana biyu bayan wata budaddiyar wasikar da wasu fitattun ‘yan arewacin Najeriya suka rubutawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin majalisun dokokin kasar a kai.

Fitattun mutanen sun gargadi hukumomin Najeriya da su kaucewa daukar matakin amincewa da bukatar wadannan manyan kasashe na girke sojojin su a Najeriya da zummar yaki da ta’addanci, bayan ficewar su daga kasashe irin su Nijar da Chadi.

Wasikar dake dauke da sanya hannun mutane irinsu Farfesa Abubakar Sadiq Muhammed da Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Jibrin Ibrahim da Awwal Musa Rafsanjani da kuma Dr Y.Z. Yau ta ce matakin na iya jefa yanayin tsaron kasar cikin mawuyacin hali, ganin yadda zaman su a Jamhuriyar Nijar bai haifar da da mai ido ba, saboda haka suke gargadin Najeriya wajen karbar sojojin na Amurka da Faransa.

Ministan yada labaran ya bukaci jama’ar kasar da suyi watsi da labarin wanda ya bayyana shi a matsayin na kanzon kurege.

Idris yace gwamnatin Najeriya a halin yanzu bata tattunawa da wata kasar waje, kuma bata karbi wani tayi mai kama da haka ba domin kafa sansanin soji a cikin kasar.

Ministan ya kuma kara da cewar Najeriya na ci gaba da samun hadin kai daga kawayen ta na duniya wajen tinkarar matsalar tsaron da ya addabe ta, kuma shugaban kasa na jajircewa wajen ganin an samu hadin kan domin tabbatar da tsaron kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.