Isa ga babban shafi

APC da NNPP za su yi gagarumar zanga-zanga rana guda a Kano

Ana zaman dar-dar a jihar Kano ta Najeriya sakamakon yadda manyan jam'iyyun jihar guda biyu wato APC da NNPP suka tsayar da Asabar a matsayin ranar da dukkannin bangarorin biyu za su gudanar da wata zanga-zanga a jihar.

Hotun gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da kuma abokin karawarsa a kotu Dr Nasiru Gawuna.
Hotun gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da kuma abokin karawarsa a kotu Dr Nasiru Gawuna. © RFI/HAUSA
Talla

Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na korar gwamna Abba Kabir Yusuf daga kujerarsa tare da ayyana Nasir Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris da ya gabata.

A lokacin da yake yi wa manama labarai bayani a birnin Abuja, Darekta Janar na Yakin Neman Zaben Gawuna da Garo, Rabi'u Sulaiman Bichi, ya ce, lallai za su gudanar da tasu zanga-zangar a rana guda da ita ma NNPP za ta yi makamanciyar gagarumar zanga-zangar.

Bichi ya ce, bayanan da suke samu na nuni da cewa, masu ruwa da tsaki na NNPP sun tsayar da ranar Asabar ce don gudanar da zanga-zangar jim kadan da ganawarsu da jagoransu, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Bichi ya ce, su ma za su fito ne domin nuna goyon bayansu ga dan takararsu wato Gawuna na APC.

Idan za a iya tunawa, a ranar Laraba da ta gabata ne, Kotun Daukaka Karar ta jaddada cewa, ta kori Abba Kabir Yusuf daga kujerarsa bayan wani rudani da ya barke jim kadan da fitowar takardar kotun wadda ke nuna cewa, Yusuf  din ne ya lashe zaben.

Kodayake kotun ta ce, kuskure a ka samu wajen buga takardar, lamarin da ya dada dagula rikicin siyasar jihar ta Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.