Isa ga babban shafi
ZABEN NAJERIYA

Kotun koli ta tabbatar da zaben gwamnonin Kaduna, Nasarawa, Gombe da Ogun

Najeriya – Kotun koli a Najeriya ta amince da nasarar da gwamnonin Kaduna da Gombe da Nasarawa da Kebbi da Delta da kuma Ogun suka samu, matakin da ya nuna cewar zasu ci gaba da zama a kujerunsu na kusan shekaru 3 da rabi nan gaba.

Inuwa Yahya ya zama sabon shugaban gwamnonin arewacin Najeriya
Inuwa Yahya ya zama sabon shugaban gwamnonin arewacin Najeriya © RFI/bashir
Talla

Alkalan kotun a hukunce hukunce daban daban da suka gabatar yau juma’a sun yi watsi da kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa gwamnonin nasarar da suka samu.

Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta jagoranci tawagar alkalai guda 5 wajen watsi da karar da Jibrin Barde na Jam’iyyar PDP ya gabatar a kan zaben Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahya.

Har ila yau, mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta tabbatar da nasarar gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule na jam’iyyar APC, yayin da ta kori karar David Ombugadu na jam’iyyar PDP.

Dangane da zaben jihar Kaduna, Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun tace jam’iyyar PDP ta gaza gabatar da kwararan shaidun zargin cin hanci da kuma kin mutunta dokar zabe da tace anyi, abinda ya sa ta tabbatar da nasarar zaben Sanata Uba Sani, a matsayin zababben gwamnan jihar.

Mai shari'a Uwani Abba-Aji ta amince da nasarar gwamnan Kebbi Nasiru Idris na jam'iyyar APC ya samu, yayin da tace 'dan takaran PDP Janar Aminu Bande ya gaza gabatar da shaidun da zai sa a soke zaben, saboda haka tayi watsi da kararsa.

Abba-Aji tace masu gabatar da karar sun kasa gabatar da shaidun zargin gabatar da takardun bogi da ake yiwa mataimakin gwamna Abubakar Tafida.

A wani bangare kuma, álkali Inyang Okoro ya yi watsi da kalubalantar nasarar gwamnan Delta na jam’iyyar PDP, Sheriff Oborevwori da ‘dan takarar APC Ovie Omo-Agege ya gabatar, yayin ya tabbatar da nasarar da PDP ta samu.

Alkali Okoro ya kuma sake tabbatar da nasarar gwamnan Ogun, Dapo Abiodun na jam’iyyar APC, tare da korar karar da Ladi Adebutu na jam’iyyar PDP ya shigar.

Yayin da yake tsokaci a kan nasarar da suka samu a kotu, gwamnan jihar Gombe kuma shugaban gwamnonin arewacin Najeriya, Muhammadu Inuwa Yahya yace nasarar ta tabbatar da abinda masu zabe suke so, yayin da ya sha alwashin ci gaba da jaircewa domin yiwa jama'a aiki.

Yahya yace ganin an kawo karshen shari'ar, abinda zai mayar da hankali a kai shine bunkasa ci gaban jihar sa ta hanyar gudanar da ayyukan raya kasa da kuma aiwatar da manufofin da zasu inganta rayuwar jama'arsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.