Isa ga babban shafi

Tsohuwar ministar Buhari ta nemi alkalai su mata aikin gafara

Najeriya – Tsohuwar ministan kula da harkokin mata a Najeriya, Pauline Tallen ta nemi gafarar bangaren shari’a sakamakon mummunar sukar da ta musu dangane da hukuncin shari’ar zaben fidda gwanin jam’iyyar APC da kotu ta yanke a kan Sanata Aishatu Dahiru Binani, ‘yar takarar gwamnan jihar Adamawa.

Pauline Tallen
Pauline Tallen © @Premium Times
Talla

Tallen wadda ke rike da minista a gwamnatin Buhari lokacin ta bayyana hukuncin hana Binani a matsayin mara inganci.

A baya bangaren shari’a ta hannu shugaban lauyoyin Najeriya, Yakubu Maikyau ya nemi Tallen ta janye kalamanta dangane da hukunci amma tasa kafa ta shure bukatar, abinda ya sa suka ruga kotu domin neman ladabtar da ita.

A watan Disambar bara, babbar kotun Abuja ta hukunta tsohuwar ministan, inda ta haramta mata rike duk wani mukami na gwamnati, har sai ta wallafa neman afuwa daga bangaren shari’ar a jaridun Najeriya a cikin kwanaki 30 na zartar da hukuncin.

A farkon wannan shekara, Tallen ta ruga kotu domin kalubalantar hukuncin saboda abinda ta kira rashin fahimtar kalaman nata da kuma rashin yi mata adalci.

Daga bisani tsohuwar ministar ta rubuta wasikar neman gafarar da kuma bayyana cewar ita bata nemi a bijirewa alakali da lauyoyi saboda kin baiwa Sanata Binani nasara a shari’ar tsayar da ‘dan takarar gwamnan jihar Adamawa ba kamar yadda ake fadi.

Saboda haka Tallen ta nemi gafarar bangaren shari’a da kuma ‘yan Najeriya akan kalaman nata, yayin da ta sake jaddada cewar ba’a fahimci abinda take nufi bane, kuma ba aniyarta ce ta ci zarafin bangaren shari’ar ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.