Isa ga babban shafi

Dalilan da suka sanya naki gabatar da shaidar kammala karatu na na Sakandare - Buhari

Najeriya – Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce da gangan yaki bada takardar shaidar kammala karatun sakandaren sa lokacin takarar zaben shekarar 2015 duk da cece kucen da jama’a suka yi tayi a fadin kasar.

Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Buhari yace ya gano inda ya aje takardar shaidar kammala karatun sakandaren a shekarar 2018, amma yayi kememe wajen gabatar da shi domin hana masu zargin sa samun damar ci gaba da tsokaci a kai.

Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo da A'isha Buhari da Tinubu na kallon yadda ake nishadantar da baki a yayin bikin rantsuwar.
Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo da A'isha Buhari da Tinubu na kallon yadda ake nishadantar da baki a yayin bikin rantsuwar. © Nigeria presidency

Tsohon shugaban yace abune da bai zai yiwu ba ya tafi kasar India yin karatu a cibiyar horar da kananan hafsoshin sojin kasar a shekarar 1973 da kuma cibiyar horar da dabarun yaki ta Amurka idan bai mallaki takardar shaidar da ake magana a kai ba.

Buhari yace a lokacin da suka yi makaranta yana da wahala a samu masu aikata laifuffukan satar jarabawa ko kuma mallakar takardun bogi.

Tsohon shugaban yace shi da abokansa da suka yi karatu na shekaru 9 a firamare da sakandare, cikin su harda Janar Shehu Musa Yar’Adua sanda suka rubuta jarabawa kafin samun damar shiga makarantar soji.

Buhari yace sanda aka gwada su a fannin Turanci da Lissafi da kuma bangaren ilimin bai daya.

Wadannan bayanai na tsohon shugaban kasar na kunshe ne a cikin sabon littafin da mai bashi shawara a kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya wallafa aka kuma kaddamar a makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.