Isa ga babban shafi
Jibiya

Yara 7 sun mutu a turmitsitsin kokarin tserewa 'yan bindiga

Kananan Yara 7 sun rasa rayukansu, wasu mutanen da dama kuma sun jikkata sakamakon turmitsitsin da ya faru a kauyen Shimfida da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Yan bindiga a Najeriya.
Yan bindiga a Najeriya. © Daily Trust
Talla

Wani mazaunin yankin da muka tuntuba da wayar tarho ya tabbatar mana da aukuwar lamarin, inda yace mutanen sun shiga tashin hankalin ne, sakamakon fargabar harin 'yan ta'adda ke shirin kai musu, abinda ya tilasta musu kokarin tserewa a ranar Alhamis.

Majiyar tamu ta shaida mana cewar ‘yan bindigar sun samu kwarin gwiwar afkawa mazauna kauyen na Shimfida ne bayan da aka janye sojojin da ke cikin rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro da ke yankin.

Gungun ‘yan bindigar sun fara kora mata kenan, su ka hango jerin gwanon motocin da suka zaci na jami’an tsaro ne, abinda ya sanya suka tsere.

Mazaunin yankin garin na Jibia ya shaida mana cewar a halin yanzu kimanin mutane dubu 10 suka tsere daga garin na Shimfida saboda fargabar hare-haren na ‘yan bindiga, inda wasu suka tsallaka Jamhuriyar Nijar, wasu suka kwarara zuwa cikin garin Jibia, yayin da wasu suka fantsama zuwa wasu yankunan a cikin Najeriya.

Wasu sabbin bayanai kuma na cewa bayan tserewar da mutanen suka yi, ‘yan bindigar sun sake komawa kauyen inda suka sace kayayyakin abinci da sauran nau’ika dukiya mai tarin yawa, tare da yin awon gaba da wani adadi na mutanen da basu samu damar barin muhallansu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.