Isa ga babban shafi
Najeriya-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun yi awon gaba da sama da mutane 50 a Katsina

'Yan bindiga a Najeriya sun sake sace akalla mutane 50 a kauyen Ruwan Godiya dake karamar hukumar Faskari a Jihar Katsina, sakamakon wani kazamin harin da suka kai garin.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Jaridar 'Daily Trust' cewar ‘yan bindiga sama da 60 bisa babura suka je garin inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Mutumin ya ce ‘yan bindigar sun kwashe sama da awa 2 suna cin karensu babu babbaka, inda suka kwashe dukiyoyin jama’a ciki har da kayan abinci da tufafi kafin su kora jama’a.

Jihar Katsina, wadda take jihar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito na ci gaba da fuskantar munanan hare hare daga 'yan bindiga, wadanda ke halaka jama’a ba tare da kaukautawa ba.

Ko a karshen makon da ya gabata sai da 'yan bindigar suka kashe mutane 11 a karamar hukumar Ilela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.