Isa ga babban shafi
Najeriya - Katsina

'Yan bindiga sun sake tsananta kai hare-hare a wasu sassan Katsina

Mazauna yankunan da ke kan hanyar da ta tashi daga garin Funtua zuwa Shema a jihar Katsina, sun gudanar da zanga-zanga inda suka datse babbar hanyar a ranar Laraba, domin nuna bacin ransu akan yadda hare-haren ‘yan bindigar da ke karuwa a yankunan nasu.

Wasu 'yan bindiga a Najeriya.
Wasu 'yan bindiga a Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Bayanai sun ce zanga-zangar lumanar ta katse hanzarin matafiya da dama da lamarin ya rutsa da su tsawon lokaci, kafin daga bisani su samu wucewa.

Zanga-zangar lumanar dai ta biyo bayan wasu hare-hare da gungun ‘yan bindiga suka kai a baya baya nan, ciki har da na kauyen Kwakware, inda suka sace mutane fiye da 10, akasarinsu mata a farkon mako, da kuma kashe wani direba da suka yi tare da kone shi a cikin motarsa.

A ranar Talata kuwa mutane 7 ‘yan bindigar suka kashe tare da sace wasu 5, a kusa da wani shingen jami’an tsaro da ke karamar hukumar Faskari, kamar yadda mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Shehu Dalhatu Tafoki ya shaidawa jaridar Daily Trust a Najeriya.

Katsina na daga cikin jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da hare-haren ‘yan bindiga, musamman a yankunan karkara da kuma wasu manyan hanyoyinta.

Sai dai gwamnatin Najeriya da hukumomin tsaronta na bayyana cigaba da kokarin murkushe matsalar tsaron ta hanyar daukar matsakan da suka dace.

Ko a baya bayan nan, rahotanni sun ce rundunar sojin Najeriya ta fatattaki ‘yan bindiga tare da kashe da yawa daga cikinsu a kauyen Katanga dake jihar Sokoto, lamarin da ya tilastawa kasurgumin dan fashin daji Bello Turji neman sulhu da gwamnati.

Sai dai a yayin da hukumomin tsaron Najeriyar ke kaddamar da hare-hare kan ‘yan bindigar a wasu sassan dazukan na yankin arewa maso yammaci, wasu na ba da shawarar cewa, kamata yayi hadin gwiwar hukumomin tsaron su kaddamar farmaki akan ‘yan ta’addan a dukkanin dazuka ko yankunan da suke boye a lokaci guda, gami da datse musu dukkanin hanyoyin tsira, domin kawo karshen matsalar tsaron da ta ki ci ta kuma ki cinyewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.