Isa ga babban shafi
Katsina-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun saki Basaraken gargajiya da mutane 35 bayan biyan miliyan 26

‘Yan bindiga a Najeriya sun saki wani Sarkin Kauyen Guga da ke karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina, Alhaji Umar tare da wasu mutane 35 da suka yi garkuwa da su na kwanaki 29 bayan da 'yan uwan su suka biya kudin fansar da ya kai naira miliyan 26.

'Yan bindiga sun addabi jihohin Zamfara da Katsina a Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi jihohin Zamfara da Katsina a Najeriya. © dailypost
Talla

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari kauyen su ne a ranar 7 ga watan Fabararirun da ta gabata, inda suka kashe mutane 10 kafin dauke wasu 36 cikin su harda Basaraken garin.

Kwanaki biyu bayan dauke mutanen, ‘Yan bindigar sun bukaci a biya su diyyar naira miliyan 30 kafin su sako su, abinda ya sa jama’ar kauyen suka dauki lokaci suna ciniki da su domin amincewa da kudin da zasu iya biya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewar, bayan doguwar tattaunawa, ‘Yan bindigar sun amince su karbi naira miliyan 10 amma kuma da aka kai musu sai suka ce sun karba ne a matsayin diyyar ‘Yan uwansu da aka kashe, saboda haka sai an karo miliyan 20.

Abdullahi Umar wanda ‘da ne ga Basaraken yace dole suka koma suka sayar da wasu kadarorin da suka mallaka inda suka tara naira miliyan 16 suka kuma kai musu a karshen mako, yayin da Yan bindigar suka saki mutanen da yamma.

Umar ya bayyana cewar kowanne mutum dake garin, ciki harda wadanda ba’a dauki Yan uwan su ba, sun bada gudumawa wajen tara kudin fansar da aka kai wa barayin.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da 'yan bindiga suka hana jama’ar ta sakewa domin gudanar da harkokin yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.